Buhari Nason Amaechi Da Lawan Ne Za Su Gaje Shi---Sule Lamido

Buhari Nason Amaechi Da Lawan Ne Za Su Gaje Shi---Sule Lamido
 

Babban jagoran jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya ce yana hasashen juyin mulki a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Lamido ya ce wannan juyin mulki ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi. 

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard. 
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya yarda cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne kadai dan takarar shugaban kasa na APC da zai iya ba jam’iyyarsa ta PDP ciwon kai. 
Sai dai kuma, ya ce Tinubu ba zai taba zama dan takarar jam’iyyar mai mulki ba a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023. A makon da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na PDP. Lamido ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa ba saboda tunaninsa.