Abin Da Ya Sa Naira Ta Shiga Cikin Sahun Kudi Mafi Rashin Daraja a Duk Afrika

Abin Da Ya Sa Naira Ta Shiga Cikin Sahun Kudi Mafi Rashin Daraja a Duk Afrika

 

Babban bankin Duniya ya kawo kudin Najeriya na Naira a cikin kudin da darajarsu su ka fi kowane karyewa a Afrika. The Cable ta ce darajar Naira da kudin Angola watau Kwanza ya na karyewa sosai, sun zama abin Allah-wadai a nahiyar Afrika. 

A shekarar 2023, Naira da Kwanza sun rasa kusan 40% na darajarsu a sakamakon dalilai da-dama.
Babban bankin ya ce matakin da bankin Najeriya na CBN ya dauka na cire takunkumi wajen kasuwanci ya nakasa Naira.
A ranar Larabar nan ne bankin duniyan ya fitar da rahoton kasashen Afrika kamar yadda ya saba yi sau biyu a kowace shekara. 
Karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya da yawan bashi da ake bin Angola ya taimaka wajen karya Kwanga. Sauran kudin da su ka karye a shekarar nan sun hada da fam na kasar Kudancin Sudan, Burundi Franc (BIF) da Kenyan Shilling