Jami’an ‘yan sanda 4,449 ne suka kai babban sufeton ‘yan sandan Najeriya kara Kotu
Yan sandan sun zargi rundunar sandan da babban sufetun da kin yi musu ado da sabbin mukamansu bayan da hukumar kula da ayyukan yan sanda ta amince da karin girman,
Kotun ta ta’allaka ne kan zargin kin aiwatar da hukuncin da majalisar wakilai ta 19 ta yanke, wanda ya ba su karin girma kamar yadda dokar PSC ta tanada.
A zaman kotun da mai shari’a R.B. Haastrup ya jagoranta a ranar Talata, lauyan masu kara, Muka’ila Mavo, ya bukaci kotun da ta tilastawa rundunar ‘yan sandan Najeriya da IG su aiwatar da karin girma da aka amince da su ba tare da bata lokaci ba.
Mavo ya kawo misali da sashe na 6 (1) (a) na dokar hukumar ‘yan sanda da sashe na 16(3)(a) na dokar ‘yan sanda, inda ya bayyana cewa wadannan dokokin suna baiwa hukumar PSC ikon gudanar da nade-naden mukamai, karin girma da kuma da’a ga jami’an ‘yan sanda, ban da IG.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya