An ci zarafin yan jarida 56 a yayin zanga-zangar matsin rayuwa a Nijeriya -- CPJ

An ci zarafin yan jarida 56 a yayin zanga-zangar matsin rayuwa a Nijeriya -- CPJ

Kungiyar Kare Yan Jaridu, CPJ, ta bayyana cewa an kaiwa 'yan jarida akalla 56 hari tare da cin zarafinnsu a zanga-zangar matsin rayuwa mai taken #EndBadGovernance a fadin Najeriya.

Ƙungiyar, mai rajin kare hakkin 'yan jarida a fadin duniya ta kuma nuna damuwar ta kan yadda ake samun karuwar cin zarafin masu aikin yada labarai a Najeriya da sauran kasashen Afirka.

A cewar wani rahoto da ta buga a shafinta na yanar gizo a jiya Laraba, CPJ ta ce rahoton ya dogara ne kan hirar da ta yi da wadanda abin ya shafa, da rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida, da kuma ingantattun shaidu na gani.

Ta kuma nuna takaici kan yadda rundunar ƴansanda a jihohi da dama suka rika musanta rahotannin cin zarafin ƴan jaridar, inda wasu kuma su ka ki bada bayanai ga kungiyar