Tinubu Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Katsina Shugaban  TETFund

Tinubu Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Katsina Shugaban  TETFund

 

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, a matsayin sabon shugaban majalisar gudanarwa ta TETFund. 

Aminu Bello Masari, tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya ya yi gwamnan Katsina na tsawon shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023. 
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren ranar Talata. 
Gwamna mai ci, Malam Dikko Umaru Radda shi ne ya gaji Masari a Katsina bayan samun nasara a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris, 2023. 
Mista Ngelale ya ƙara da cewa shugaban ƙasar ya kuma naɗa wasu mutum shida a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta asusun kula da manyan makarantu TETFund. 
Sun hada da Sanata Sani Danladi, Sunday Adepoju, Nurudeen Adeyemi, Esther Onyinyechukwu Ukachukwu, Turaki Ibrahim da kuma Aboh Eduyok. 
Shugaba Tinubu ya buƙaci sababbin mambobin gudanarwa na TETFund da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya.