Gwamnatin Kaduna ta ware biliyan 3.1 don biyan fansho da garatuti a Jihar
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya amince da ware naira biliyan 3.1 domin biyan garatuti ga ma'aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan ma'aikatan da suka mutu.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya ce hakan na daga cikin manufofin gwamnan na rage wahalhalun da tsoffin ma'aikatan ke fuskanta, waɗanda ke cikin mutanen da suka fi shan wahalar rayuwa a jihar.
Sanarwar ta ce gwamnan na son tabbatar da cewa tsoffin ma'aikatan jihar sun samu haƙƙoƙinsu kamar yadda doka ta tanadar.
''Gwamnatin jihar Kaduna ta hanyar hukumar biyan Fansho ta jihar za ta tabbatar da ci gaba da biyan kuɗaɗen fanshon ga tsoffin ma'aikata da kuma iyalan ma'aikatan da suka mutu a faɗin jihar'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Gwamnatin Kaduna ta ce waɗannan kuɗaɗe za su taimaka wajen warware wa mutane matsalolin matsin tattalin arziki da suke ciki, musamman tsoffin mutanen da suka bar aiki.
managarciya