Karimci: Gwamnan Nasarawa Zai Biya Ma'aikata Sabon Albashin Dubu 70 

Karimci: Gwamnan Nasarawa Zai Biya Ma'aikata Sabon Albashin Dubu 70 
 
Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule zai fara biyan ma'aikatan jiha sabon abashi mafi karanci na 70 a watan Agusta.
Gwamnan a wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta ya ce zai biya ma'aikatansa ariyas tun daga watan Mayu domin shi a wurinsa za a soma biyan sabon albashi ne daga watan na Mayu shi ne ka'ida.
Gwamna ya ce za a fara biyan ma'aikata ariyas na watannin da suka gabata, watan Mayu da Yuli da Juli kafin soma biyan sabon albashin a watan Agusta.
Wannan karimci ya faranta rayuwar ma'aikatan jiha da kasa baki daya domin halin matsi da kunci da al'umma suke ciki saboda hauhawar farashin kayan masarufi.