Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna
An bayyana cewar tavarvarewar tarbiyar matasa da ya janyo suna anfani da makamai wajen kaiwa al'umma hare hare suna sata cikin garin Minna a qaramar hukumar Chanchaga laifin iyaye ne na rashin kulawa da haqqin tarbiya kamar yadda addini ya xora masu. Tsohon shugaban qungiyar malaman makarantun tsanya da almajirai a jihar Neja kuma Ambasadan zaman lafiya, Ambasada Musa Adamu ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna.
Shehin malamin ya cigaba da cewar wasu gurvatattun mutane ne suka shigo da yahudanci iyaye suka runguma suka ratayawa kawunan su, wanda sakaci da saken da ake yiwa tarbiyar 'yaya ya jefa su a irin wannan halin da ake ciki yanzu, amma yadda za a yi a ce gwamnati na faman yaqi da 'yan ta'addar da suka mamaye yankunan karkara, kuma a bar wasu gungun matasa da sunan daba har suna yunqurin hana wasu 'yan unguwanni shiga unguwannin su.
Abin baqin ciki da takaici, yaro ya xauki makami ya kashe shi ba tare da laifin komai ba, wai dan ya shiga unguwarsu kuma ya samu jama'a a maqabarta ana binne wanda ya kashe yayi yunqurin tarwatsa jama'a, wannan wani irin rashin imani da hankali ne, ya zama dole duk matashin da aka samu da sunan daba ko ta'addanci jami'an tsaro su yi mai hukunci daidai da yadda dokar qasa ta tsara. Yaran da ake kanawa, iyayen su ne da wasu na kusa da gwamnati ke yin uwa makarviya wajen karvo belin su.
Ina kiran iyaye da babban murya da su ji tsoron Allah, suna 'yaya amana ne a hannun su da su Allah zai tambaya amanar da ya ba su, amma ba daidai ba ne mutane su yi shiga kafafen yaxa labarai suna sukar gwamnati, duk wani abinda ya kamata a baiwa jami'an tsaro na kayan aiki, gwamnati na ba su to a ina matsalar take, duk yaron da aka samu da laifin daba kuma aka yi kyakkyawar bincike akansa aka same shi da laifi a tabbatar an hukunta shi, sannan duk wani shugaba ko uba da ya tunkari jami'an tsaro da sunan beli a tabbatar an cafke shi domin ya nuna qarara da hannunsa wannan abin ke faruwa.
Ambasada Musa, ya jawo hankalin gwamnati wajen sanya idanu da qarfafa guiwar jami'an tsaro, gami da ba su goyon baya wajen kawo qarshen wannan ta'addancin 'yan dabar na cikin garin Minna. Domin itace shalkwatan jiha, idan ta gurvace ba yadda za a samu cigaban da ake nema, babu wanda yasan ciwon kan shi da zai goyi bayan cigaba da wannan mummunar xabi'an daba da sara suka, balle yayi baqin cikin hukunta mai laifi.