Lauyan kungiyar da ke jagorantar zanga-zanga ya nemi a janye nan take
Lauyan kungiyar 'Take it Back Movement' da ke jagorantar zanga-zanga, Adegboruwa ya bukaci masu zanga-zangar da su janye inda ya bayyana kaduwa kan asarar rayuka da dukiyoyi.
A sanarwar da ya fitar a yau Juma'a lauyan ya ce ba haka suka nufa ba da shirya zanga zangar inda ya mika jaje ga wadanda lamarin ya shafa.
"Muna mika ta'aziyya ga iyalan jami'an tsaro da masu zanga-zanga da suka rasa ransu. Muna rokon Allah ya basu ikon jure rashin da suka yi".
Babban Lauyan dai shi ne ya nemi masu shirya zanga zangar da su rage kwanakin yinta zuwa kwana 1 a washegarin fara zanga zangar.
Haka kuma ya bukaci shugaban kasa Tinubu ya yiwa 'yan kasa jawabi tare da tattaunawa da wakilan masu zanga zangar.
Zanga zangar dai da aka fara a jiya Alhamis kan tsadar rayuwa ta juye zuwa rikici a wasu jihohin Arewacin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da jikkatar mutane da dama.
managarciya