'Yan Bindiga Sun Sace Mutane  15 Tare Da Babura 7 A Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane  15 Tare Da Babura 7 A Sakkwato

 

'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun shiga kauyukkan karamar hukumar Wurno dake jihar Sakkwato a cikin kwana biyu sun sace mutane 15 da babura 7 sun kashe mutum daya da jikkata daya.

Wata majiya ta shedawa Managarciya yanda wannan lamarin ya faru ya ce "a shekaran jiya alhamis maharan sun tafi garin Achida in da suka sace mutane 3, a jiya Jumu'a sun shiga garin Barayar Zaki sun sace mutane 6 tare da babura 7 na mutanen gari bayan sun kashe mutum daya.

Bayan nan sun tafi Gidan Zago suka yi garkuwa da mace 4 da namiji guda, sun biyo ta Kandam suka tafi da mutum daya kafin sun jikkita mahaifin wanda suka dauka don ya so ya hana a tafi da dansa," a cewar majiyar.

Ya ce mutanen da yawa suka taho saman babura tare da miyagun makamai suka yi wannan tu'annati mai matukar tayar da hankali.
Duk kokarin jin tabakin hukumar 'yan sandan jiha bai yiwu ba.