Daga Babangida Bisallah, Abuja.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci kungiyoyin kwadago da su yi watsi da shirinsu na yin zangar zangar kin amincewa da shirin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.
Lawan yayi kiran ne ranar Litinin yayin da yayi taro da ministan kudi, Zainab Ahmed da ministan kasa a ma'aikatar man fetur, Timipre Sylva da sauran jami'an gwamnati a kan shirin cire tallafin.
Lawan ya soki cire tallafin a cikin halin yanayin da ake ciki, yana mai cewa, duk da tsarin biyan tallafin na da matsaloli, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi amanar cewa dole ayi cikakken tsari kafin a cire tallafin.
A don haka ne, Lawan yayi kira ga kungiyoyin kwadago da suyi watsi da shirin su na zanga zangar, yana mai bayanin cewa, gwamnatin tarayya ba da shirin cire tallafin man fetur a halin yanzu.
Yace, "¹matsayin kowa a gwamnati a yau shine an yarda akwai matsaloli tattere da tsarin biyan tallafin saboda wasu dalilai masu yawa.
"An yarda cewa nauyin yana da yawa da girma kuma akwai bukatar ayi watsi da tallafin a wani lokaci.
“Duk da cewa tattalin arzikin mu yana habaka, duk da haka muna da kalubalen sama ma mutanen mu saukin rayuwa.
“Da yawan mu a cikin wannan gwamnatin mun yi imanin dole ne a yi takatsantsan akan maganar cire tallafin man fetur, musamman ma saboda bukatar yin isasshen tsari.
“Abin da muke cewa shine ba yanzu ne lokacin da ya dace ba. Dukkanin mu muna da ra'ayi iri daya, a don haka ba wani abu kamar rudu ko rashin fahinta a tsakanin gwamnati.
"Dukkanin mu mun yarda cewa ana cuwa cuwar tallafin, a don haka ya zama kalubalen gare mu a matsayin mu na gwamnati mu yi maganin wannan cuwa cuwar, a samar da hanyoyin da suka kamata na kawo karshen ta".
A jawabin ta, minister kudi, Zainab Ahmed tace gwamnatin tarayya tayi tanadin kudin tallafin man fetur a cikin kasafin kudin bana daga watan Janairu zuwa Yuli.
A cewar ta za'a daina biyan tallafin akan man fetur daga watan Yuli na bana.
Tace, ganin cewa lokacin da aka sa na cire tallafin yana da matsala, gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin dakatar da shirin ta na cire tallafin a watan Yuli.
Ahmed tace bangaren zartaswa zai gabatar ma majalisar dokoki ta tarayya da bukatar samar da karin kudaden tallafin daga watan Yuli zuwa lokacin da yafi dacewa a cire shi.