Wasu Boyayyun Lamurra Da Suka Bayyana Bayan Mutuwar Shaikh Giro Argungu
Shaikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu an haife shi a garin Suru hidikwatar karamar hukumar Suru a jihar Kebbi a shekarar 1961 ya bar duniya yanada shekara 62.
Yabar matan Aure 4 da diya 18 Maza 11 mata 7 da jikoki 24 bayan kwashe shekara 10 yana fama da ciwon zuciya.
Shaikh ya rasa mahaifinsa tun yana dan shekara biyu dalilin da ya sa ya dawo wurin yayan mahaifinsa a garin Giro anan ne ya cigaba da daukar dawainiyarsa a matsayinsa na maraya, acikin garin ne aka sanya shi makarantar allo don fara karatun musulunci a makarantar da aka fi sani da tsangayar Liman Abubakar Sabo.
Shekararsa uku yana karatu a wurin Malam Sabo da hazakarsa ta fito fili Malam ya ga akwai bukatar ya tura shi wurin Malam Yakubu Illela shi ma a garin Giro yake da zama in da ya ci gaba da karatun yaki da jahilci.
Son ilmi da yake yi ya ba shi damar shiga Makarantar Furamare Giro Argungu anan ya kammala bai tsaya ba ya samu gurbin karatu a kwalejin koyar da malamai ta Gwamnati in da ya yi karatunsa na Sikandare.
Shaikh ya fara da'awa tun yana da shekara 19 in da ya samu shahara a Nijeriya da Afirika gaba daya kan salon wa'azinsa na kadaita Allah da bauta.
A cikin 'ya'yan margayi Kuma makusanci gare shi Wanda yake da sunan Hassan Abubakar Giro ya yi wa manema labarai bayani kan yadda rasuwar margayin ta same su shi da 'yan uwansa da mahaifansa, "a cikin yaran da mahaifinmu ya bari a manya ni ne na hudu, kasan dukan rayuwa za ta mutu amma akwai ciyo na rabuwar mahaifi musamman wanda kake kusa da shi, ba zan iya misilta Maka yanayin da na shiga gaskiya, ni ke kula da komai nasa hasalima nafi kusanci da shi dani ake tsara tafiye-tafiyensa duk dare da rana Muna tare.
"A daren Laraba da da ciwon sa ya tashi muna tare da shi ba zan manta ba bayan ya gama karatu sai ya tafi ya kwanta yana kallon sunnah TV Kano, dana shigo wurinsa ya ce na zuba masa maganinsa ya sha naje daukar maganin ashe ya kare nan take ya umarce ni naje na sayo masa maganin, bayan na dawo na zuba masa maganin ya sha, sai na zauna muka yi tsarin duk abin da yakamata har da tafsirin da zai yi ranar Laraba, anan ya ce min sai da safe na tashi na fita, ban yi minti 30 ga Malam nan ya fito zai fadi, daga nan aka dauke shi zuwa Clinic anan Argungu aka kwantar da shi anan ne yana amai(haraswa) ya ji sauki abin ya dawo haka ake har Asuba sai ya samu sauki ya yi sallar Asuba ya kwanta dana ga sauki ya samu sai na bar wurin.
"Wuraren karfe 7 na safe abin ya dawo masa sai aka tafi da shi Asibitin Birnin Kebbi ba dani aka kai shi ba don na tafi gida na shirya saboda asibiti na kwana, ko dana tafi na samu an sa masa Oxygen injimin tallafin iska daga nan hankalina ya tashi na kasa zama wurinsa, kusan la'asar aka yi shawarar mayar da shi Sakkwato a kwantar da shi kusan magrib an kawo motar daukar maras lafiya an sa shi ne sai ya yi magana ya ce zuciyar shi yana son ya tashi a haka fa Allah ya yi masa cikawa," ya fadi yana zubar da hawaye.
Malam ya shafe wane lokaci yana fama da wannan ciwon zuciya? ya ce Malam ya kwashe shekara 10 ko fiye da ciyon tun zuwansa Egypt na farko kan ciwon ne bayan ya yi kwanci asibitin koyarwa ta Danfodiyo a Sakkwato a haka ne duk shekara daya ko biyu yakan tafi can don duba lafiyar, wannan shi ne zaman da ya yi a UDUTH ma ciyon ne da Maleriya."
Malam yabar gibi sosai a Nijeriya da Afrika wane abu kuke ganin za a yi don sanyaya rashinsa? ya ce "a gaskiya a tarihin rayuwata ban taba ganin mutum Mai kyauta kamar Malam ba don harkar kudi ta gefe na nasan da yawan gaske Malam nada lalurar kudi dubu 100 ya same su wani ya zo masa da bukatar dubu 100 ya mika masa su ya zauna haka nan bai yi tasa bukatar ba, ka ga samun Mai wannan halin da wuya cike gibinsa kullum abin da yake nuna mana mu rike addininmu da gaskiya kar mu yi wasa da addini, ba za mu manta da Malam ba kullum yana nuna mana mu bi rayuwa a hankali duk yanda ka dauke ta haka za zo maka, ya yi min wasiya sosai. A duk dare sai na sawo masa Kankana da Lemu domin likita ne ya ba da shawarar ya rika shan 'ya'yan itace shi kuma yafi son Kankana da Lemu duk sanda naga Kankana da Lemu zan tuna da Mahaifinmu."
Mi Malam ya bari? "yana da Makarantar Islamiya da Furamare sunan Makarantar Shaikh Abubakar Giro Nursery and Primary School, tun da na tashi na samu Makarantar," bayanin Hassan Giro.
Kabiru Haruna Gombe sakataren kungiyar IZALA ya nuna yanda aka yi rashin Giro ya ce bayan Allah ba wanda yasan kasar da Giro ya taka zuwa wa'azi a Afrika, Sakkwato da Kebbi da Neja sun fi cin gajiyar Malam.
"Malam ya taka rawa sosai a rayuwata duk aure uku dana yi ba Wanda bai ba da gudunmuwarsa sosai ba, Malam na cikin malaman Sunnah daga Nijeriya da kasar Nijar da Ghana da Kwadibuwa suka fara sani ban tsammanin akwai in da bai taka ba a Nijar, mutwar Malam masifa ce a cikin al'umma, ranar da Malam ya rasu da dare Malam Abbas Jega ya kirani domin yimin ta'aziya Yana can kwance a asibiti a Kano saboda kauna ta addini ya ce ji yake kamar a ce Malam Giro bai mutu ba, Allah na yi wa malaman suñnah gata a karshen rayuwarsu," a cewar Kabiru Gombe.
Shaikh Abubakar Salihu Zariya ya ce duk Mai imani a Nijeriya zuciyarsa ta sosu ga mutuwar Shaikh Giro Argungu "ba zan manta ba kafin IZALA ta hade Muna bangaren Kaduna a lokacin da aka fara a zani mimbarin wa'azin Kasa Malam Giro ya kirani a masauki ya yi min nasiha kan yin abu don Allah da yin hakuri da mutane. Ban mantawa kudi da mutum zai samu ya ce ya samu kudi(masu tsoka) Wanda na fara samu a rayuwata Giro Argungu ne sanadi.
"Malam aiyukkansa na alheri ba su kidayu ba tsakani da Allah, muna fatan Allah ya gafarta masa. Da dama wasu malamai ba ruwansu da taimakon dan uwansu bayan ya rasu kar a yi wa Malam haka. Shawarata ga diyansa su kare martabar Malam su yi hakuri da junansu su so juna, mawadata su yi abin da za za su iya," Kalaman Salihu Zariya.
Shaikh Suleiman Bawa Argungu shi ne wanda Giro ya ba da wasicin ya gade shi a wurin karance karancen da yake yi a hirarsa da wakilinmu ya ce "gaskiya mun ji a jikinmu kwarai da gaske kan rasa Malam kusancinmu gare shi an mayar da mu marayu mun rasa uba, jagora, mun yi kuka kan rashinsa, sai dai abin da ke sa mu farinciki Malam ya gama lafiya dimbin jama'ar da suka zo wurin janazarsa ke nuna hakan Allah ya gafarta masa."
Da an kira Malam mi kake tunawa da shi? ya ce " tau abubuwa dama nake tunawa duk sanda na ji wa'azinsa ko aka ambace shi ko a aka yimin ta'aziyarka gaskiya na jima Ina jin kamar mafarki nake yi kan Malam ya rasu, nakan tuna aiyukkan dake gabanmu musamman wurin shirya taro don wurinsa muke zuwa ya tsara mana da nema mana taimakon duk Malam ke yi amma dai Allah na nan zai taimakemu mu yi lafiya in hakan ya taso don shi ne ya ba mu Malam."
A lokacin rayuwar Malam an dauki Wani hamshakin Mai kudi ne Ashe ba haka ba kana ganin rayuwar ta dace da Malam? ya ce " tau gaskiya ko mu Muna ganin bai dace ba shi haka ya zabar ma kansa, ina tabbatar maka ko da Malam yabar duniya babu dubu 10 a cikin asusun ajiyar bankinsa ko ya samu kudi mutane yake rabewa sai ka ga ya yiwa mutane lalura ta makudan kudade wadda bai yiwa kansa ba, mafiyawa in sun ga Malam ya sawo riga sai su za ci akwai kudi mu da muke da kusanci da shi mun San lalura takan taso gidansa babu kudi ban San adadin tambayarsa kudin cefane a gida ba amma ya ce a dai Jira, Malam rayuwarsu ba ta aje kudi mutane yake yi wa lalura har bashi yake ci kan mutane, malam shi ya zabarwa kansa rayuwar da yake yi, mu Muna jin zafinta amma shi ya saba shi manomi ne sana'arsa kenan.
"Ko gwamnati ta yi abin da Malam ke za ta ji jiki wata ran ana iya samun matsala, duk abinda ka ga Malam ya yi mutane ne yake yiwa ba kansa ba, duk Wanda ka ga yabi Malam bashi wasu ne aka yi lalura Malam ya dauka masu binsa bashi aminansa ne Kuma an biya, ba Wanda ke biyar Malam bashi a saninmu. Ita kungiya ta yi abin da take iyawa Kuma Malam bai taba kawo mana sukar kungiya ba, mutum ne mai zurfin ciki, IZALA ce ta dauki nauyin zuwansa asibiti na farko Dana biyu, ko wannan da ta taso shekararsa ta zuwa asibiti bai yi ba ne don har Shugaban IZALA na kasa ya shirya in lokaci ya yi ya koma a duba lafiyarsa Allah ya kaddari nan ne za a karbi ransa.
Wasiyar Malam Kai ne za ka jagoranci karance-karancen da yake yi mi za ka ce kan wannan nauyin? ya ce "wasici ne ya bari amma nasan irin kujerar da Malam ke hawa da irin yanda mutane ke son su ga Malam nasan ni ban da wannan kwarjini da haibar ina rokon Allah mutane su taya ni addu'a na yi ko daya cikin 100 na aiyukkansa nasan ba zan yi kama da shi ba, Allah ne ya sa ya fade ni a cikin wadanda suka fi ni karatu da shekarru da muke tare da su da Malam, tun da yace ni ya daura min aikin wanda yake babba domin kujerarsa wuyar hawa gare ta, kana gani shugaba na kasa da sakatare sun ce aiyukkansa su kansu wahala yake ba su duk suka an shiga damuwa Malam baya da lafiya kenan, ina rokon Allah ya bani damar in yi wani abu bisa ga wasicin Malam",Kalaman Argungu Kenan.