Shugaban  PDP Na Ƙasa Ya Naɗa  Yusuf Dingyaɗi Babban Mai Taimaka Masa  A Harkokin Yaɗa Labarai Da Sadarwa

Shugaban  PDP Na Ƙasa Ya Naɗa  Yusuf Dingyaɗi Babban Mai Taimaka Masa  A Harkokin Yaɗa Labarai Da Sadarwa
Daga Aminu Amanawa a Abuja.
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Iyochia Ayu ya nada Alhaji Yusuf Dingyadi a matsayin babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da sadarwa.
Nadin Dingyadin dai na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan watan  26, ga watan Yuli 2022, kuma take da rattabawar hannun babban sakataren jam'iyyar na kasa, Senator Samuel N Anyanwu da bayanin yace tuni da nadin nya soma aiki tun 1 ga watan Yulin shekarar nan.
Dingyadi, wanda kwararren dan jarida ne kafin nadin nasa yayi aiki da kafofin yada labarai daban daban kafin tsunduma harkokin siyasa.
Inda yayi aiki da kafar yada labaran BBC Hausa, da kuma jaridar Nasiha da ake wallafawa a Kaduna da dai sauran su.
Yusuf Dingyadi ya kasance mai taimakawa 
margayi Abubakar Koko (Sarkin Yakin Gwandu), a kan kafofin yada labarai, dama tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa da ma gwamna maici yanzu Aminu Waziri Tambuwal.
Bayan tsunduma harkokin siyasa Yusuf Dingyadi yayi zama kakakin jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, sakataren rikon kwaryar jam'iyyar PDP a jihar Kebbi da dai sauransu.