Dakarun Operation Safe Haven sun kashe wasu kasurguman masu garkuwa da mutane biyu sannan sun kama masu fashi da makami biyu tare da ceto matafiya tara a yankin arewacin kasar.
Daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, Channels TV ta rahoto.
Ya yi bayanin cewa sun samu nasara a ayyukan da suka gudanar tare da jami’an yan sanda a tsakanin Alhamis da Asabar na makon da ya gabata a kokarinsu na ganin an yi bikin sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A cewar kakakin rundunar sojin, wadanda ake zargin sun kuma bayyana wani Mallam Buhari Umar a matsayin shugaban kungiyarsu.
Yan bindigar sun farmaki gidan Reverend Daniel Umaru na cocin EYN a Njairi da ke karamar hukumar Mubi inda suka harbe shi sannan suka kashe yaransa biyu da kuma sace diyarsa mai shekaru 13.






