Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Makashin Hanifa

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Makashin Hanifa

     

•Kotun ta sami Abdulmalik Tanko da laifin g garkuwá da Hanifa, da laifin kísanta da kuma laifin kitsa yadda za a yi garkuwá da ita.

•Kotu ta sami Hashimu Isyaku da laifin haɗa kai wajen kísan Hanifa da ɓoye laifin aikata garkuwá da Hanifa, sannan yana da masaniya an yi garkuwá da Hanifar.

•Kotu ta wanke Fatima Jibril daga zargin rubuta wa iyayen Hanifa wasikar sanar da su an yi garkuwá da ita. Sai dai ta same ta da laifin hannu waje yin garkuwá da Hanifa, da masaniyar an yi garkuwá da ita.

Hukuncin Da Aka Yanke

Bayan karanto laifukan da aka tabbatar wa waɗanda ake tuhumar, dukkan su sun nemi kotun da ta yi musu sassauci.

•Kotu ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kísa ta hanyar rátaya bisa laifin garkuwá da Hanifa da ɗaurin shekaru biyar a gidan gyaran hali na garkuwá da mutum.

•Kotu ta yanke wa Fatima hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali kasancewarta uwa.

•Ta kuma yanke wa Hashimu hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan gyaran hali sannan daga baya a káshe shi.