Sama Da Gawa 500 Ta Ɓace  a Jihar Neja

Sama Da Gawa 500 Ta Ɓace  a Jihar Neja

Daga Jabir Ridwan

Al'ummar karamar hukumar mariga dake Jahar Neja na cigaba da Neman Gawawaki akalla 500 da ake zargin ambaliyar ruwan sama tayi awon gaba dasu.

Limamin masallacin juma'a na mariga shine ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta wayar tarho a ranar talata.

Limamin yace har yanzu Basu Samun labarin inda wadannan gawawaki suka shiga ba.

Hakama limamin yace al'ummar mariga na cikin rudani kasancewar Saida suka sauyawa akalla gawawaki 100 bagire sakamakon ambaliyar ruwa.

Limamin Wanda ya alakanta ambaliyar ruwan da ayukkan masu hakar ma'adinai ba bisa qa'ida ba , yace tsawon shekaru 60 Basu fuskanci irin wanna matsala ba a maqabartar.

A karshe yayi kira ga gwamnatin jahar neja da ta gagauta daukar mataki domin shawo kan wannan matsalar.