Tambuwal Ya Sake Mayarda Aminu Bala Ma'akatar Filaye Da Gidaje A Sakkwato

Tambuwal Ya Sake Mayarda Aminu Bala Ma'akatar Filaye Da Gidaje A Sakkwato

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sake mayar da Kwamishina Honarabul Aminu Bala Boɗinga ma'aikatar filaye da gidaje ta jihar Sakkwato domin cigaba da aikinsa.
Honarabul Aminu Bala kafin ya ajiye aikinsa don yin takarar Sanata shi ne kwamishina a ma'aikatar bayan ya sadaukar da takararsa ga Gwamna, sai ya sake nada shi kujerar kwamishina ya rantsar da shi a Laraba data gabata(jiya).

Kwamishinan ya halarci taronsa na farko a wannan Alhamis  bayan tura shi ma'aikatar a Otal na Ɗankani in da aka gudanar da taron yini huɗu kan sha'anin filaye da gidaje, an samu halartar kusan dukkan kwamishinonin jihohin Nijeriya.
Gwamnan Sokoto da Ministan filaye da gidaje na Nijeriya Raji Fashola sun samu halartar taron.

Sauran kwamishinonin da aka rantsar suna jiran a tura su wuraren da za su soma aiki kowane lokaci daga yanzu ganin an tura ɗan uwansu da aka naɗa su tare.