Shugaban APC Shi ne Ya Cuci Ɗiyansa Ba Ni Ba-----Tambuwal

Shugaban APC Shi ne Ya Cuci Ɗiyansa Ba Ni Ba-----Tambuwal

 
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana yanda yake son  haɗa kai da 'yan adawa a jihar musamman magoya bayan APC amma sun ki goya mashi baya domin ciyar da jiha a gaba.
Tambuwal ya ce a duk san da aka gama  sha'anin zabe, mulki abu ne da ake hada kai domin gwamnati  ta kowa ce ga wanda ya zabe ka  da wanda bai zabe ka ba in ka yi aiki na kowa ne haka jagorancin yakamata "anan Sakkwato haka muka dauka, haka muke yi ina jin dadin yanda muke hada hannu da dan majalisar tarayya na kananan hukumomin Illela da Gwadabawa Abdullahi Balarabe Salame, a kowace jam'iya mutum yake in ya gayyace ni zan je domin al'umma ake magana kuma su muke wa jagoranci," a cewar Tambuwal.

Ya yi wannan kalamai ne a wurin rabon kayan mazaɓa na ɗan majalisar tarayyar.
Ya ci gaba da cewa "yakamata mu rage sha'anin gaba da ƙiyayya tsakaninmu abubuwan da ke damunmu sun wuce siyasa, matsalar tsaro ina ruwansa da ɗan party, sha'anin na jagoranci bai kamata a sa siyasa ba.
"a lokacin da muka ce za mu kai dalibai 200 makaranta muka ce duk wanda ya ci jarabawa a tabbatar da shi ya tafi ko ɗan APC ko PDP ne, ɗiyan Isah Achida sun ci jarabawa, na ce a barsu su tafi makarantar nan, shi ya hana masu tafiya da kansa, shi ya cuci ɗiyansa, bani na cuce su ba, ina kira ga al'ummar Sakkwato mu zauna mu haɗa kanmu, a ci gaba da kawo zaman lafiya a jiha, abin da Allah ka yi ya gama," a cewarsa.
Managarciya ta yi yunƙurin jin tabakin shugaban jam'iyar APC a Sakkwato Isah Sadik Achida amma lamarin bai yi nasara ba an kasa samunsa a waya.

Daga Muhammad Nasir.