Mutane Da Dama Sun Amfana Da Tallafin Dan Majalisar Tarayya Hon. Abdullahi Balarabe Salame

Mutane Da Dama Sun Amfana Da Tallafin Dan Majalisar Tarayya Hon. Abdullahi Balarabe Salame
Mutane Da Dama Sun Amfana Da Tallafin Dan Majalisar Tarayya Hon. Abdullahi Balarabe Salame
 
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.
 
Dan Majalisar Tarayya na jamiyyar APC, mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwadabawa da Illela Honarabul  Abdullahi Balarabe Salame  ya raba kayayyaki ga jama'arsa, a Kananan Hukumomin da yake Wakilta. 
Kayayyakin sune kamar haka; Janarito na Kanfanin MEKANO guda 3, Agwagwa da buje Kanfanin TVS guda 175, Babur kirar Bajaj guda 175, Teloli guda 185, Kayan sawa diloli guda 178.
 Gwamnan Jihar Sokoto  Aminu Waziri Tambuwal da Mataimakin sa Hon. Manir Muhammad Dan'iya da Kakakin Majalisar Dokoki ta jiha Hon. Aminu Manya Achida da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr. Muhd Saad Abubakar da sauran Jamaa sun halarci gidan Member Mai wakiltar Illela da Gwadabawa Hon. Abdullahi Balarabe Salame wanda ya rarraba kayan da ya samo ma mazabarsa.