Dawakin Tofa da yankin Kano ta arewa, ba mu da kamar Sunusi Bature----Hon. Mai Kaza

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.
Tsohon dan takarar Kansila a mazaɓar Dawanau Honarabul Abdullahi Ado Mai Kaza ya bayyana babban daraktan yada labarai da wayar da kan jama'a na gwamnatin Kano Alh. Sanusi Bature D/tofa a matsayin jigo kuma jajirtacce a yankin Kano ta tsakiya da ma jihar Kano,.
A zantawarsa da manema labarai a Kano, Abdullahi Ado Mai Kaza kuma ce DG Sunusi Bature yayi koyi ne da halin Gwamna Kano Injiya Abba Kabir Yusuf na kishi da tallafawa al'ummar Kano,
"A Harkar ta ilimi, lafiya, tallafawa ƴan jam'iyya da ma duk abinda ya shafi ciyar da dan'adam gaba, a cikin shekara 13 da mu ke a tafiyar Kwankwasiyya ba mu da haziki jajirtacce irin mai girma Sanusi Bature"
"Ba'a dade ba a Dawakin Tofa akwai marayun da ba su da yadda za su yi, Sunusi Bature da ya samu labari nan da nan ya saya masu gida ya ba su, haka kuma a satin da ya gabata ma mai girma DG ya tallafawa Makarantar Islamiyya da kuɗi fiye da miliyan daya, ire-iren waɗannan abubuwan alherin ba sa kirguwa" inji Abdullahi Mai Kaza
Daga nan ne ya yi kira da kakakin na gwamnan Kano Sunusi Bature da ya fito takararar Majalisar tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, a cewarsa in yaso jaritaccen dan majalisa Hon. Injiniya Abdulƙadir Joɓe sai ya fito takarar Sanata a yankin na mu mai albarka.