Sanata Wamakko ya yi ta'aziyar rasuwar tsohon shugaban Ƙasa Buhari 

Sanata Wamakko ya yi ta'aziyar rasuwar tsohon shugaban Ƙasa Buhari 
Rasuwar tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari abu ne da ya taba zuciya da yin  alhini domin an rasa jigo a kasa.
A wani bayani da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai ya ce Nijeriya ta yi rashin daya daga cikin shugabanni da ba ya da son kai da almumdahana, mai kishin kasa da yin magana kaifi daya.
"Mutum ne dake da nagarta wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin yi wa kasa hidima, bai taba gazawa ba."
"Mutum ne mai sauki hali da gaskiya dake da hangen nesa wanda ya kawo cigaba kan noma da samar da wutar lantarki da hanyoyin mota da jirgin kasa da tsaro tarihi ba zai manta da shi ba."
Sanata Wamakko amadadin kansa da iyalansa da jama'ar Sakkwato ya mika sakon ta'aziyar sa ga maidakin tsohon shugaban Ƙasa Aisha Muhammadu Buhari da ɗiyansa da dangi gaba daya musamman na Daura da mutanen Kataina gaba daya.
"Allah ya garta masa kurakuransa ya sa ya huta."