Daga Janaidu Amadu Doro.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce tuni ya riga ya nemi izinin Gwamnatin Tarayya kan rufe layukan sadarwar kuma ya samu amincewar Shugaba Buhari.
A cewarsa, Jami’an tsaro ke ba wa 6ata-gari bayanan sirri.
“Ina so mutanen jihar Kaduna su sani cewa ko a yau sojoji su ka ba mu tabbaci za mu iya rufe layin sadarwa,” inji shi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da gidajen rediyon jihar a daren jiya Talata.
Gwamnan ya ce, “Babu shakka ’yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuka sun dogara ne da hanyar sadarwa wurin yin magana da masu ba su bayanai da kuma dangin wadanda su ka sace don neman kudin fansa”.
Sai dai El-Rufai ya ce toshe layukan sadarwar zai takaita ne a kananan hukumomi da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Katsina inda sojoji ke ragargazar ’yan bindiga.
Gwamna El-Rufai ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa a sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa ’yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina inda aka rufe layukan sadarwa, ’yan bindiga kan tsallako zuwa wasu kananan hukumomin jihar Kaduna da ke makwabtaka da su domin su kira waya su nemi kudin fansa.
Ya bayyana cewa, “Sojoji sun ba mu shawarar rufe layukan sadarwa a wasu kananan hukumomi, amma mu na jira su bayyana mana kananan hukumomin da kuma lokacin.”
“Ba zan bayyana sunayen kananan hukumomin ba, amma su kananan hukumomin da ’yan bindiga su ka fi addaba sun san kansu.
“Amma da zarar hukumomin tsaro sun ba mu tabbaci mutane su sani cewa za mu rufe layukan sadarwa don mu ba hukumoin tsaro cikakken hadin kai su gudanar da ayyukansu a yankunan.”
Kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kajuru da Kachia dai su ne wadanda ’yan bindiga su ka fi addaba a Jihar Kaduna.
El-Rufai ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin aiki da cikawa na dabbaka matakan da ta dauka na rufe gidajen mai da kasuwanni a yankunan da ke makwabtaka da dazukan da ’yan bindiga ke zama.
Ya yi kira ga jama’a da su taimaka ta hanyar kai karar masu hada baki ko ba wa ’yan bindiga bayanai.
“Duk wanda aka gani zai sayi sinkin burodi 20 ko fiye da hakan a sayar masa amma a sanar da hukumomin tsaro.
Haka ma duk wanda ya kawo wayoyi da yawa ya na neman a yi masa cajin su shi ma a Tuhumeshi.