Masu Ruwa Da Tsaki Sun Tattauna Kan Sha'anin Almajirci Da Makarantun Allo a Jihar Sakkwato

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Tattauna Kan Sha'anin Almajirci Da Makarantun Allo a Jihar Sakkwato
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto. 
 

A  Lahadi 4 ga watan Satumba 2022 wanda ya yi dai-dai da 7ga watan Safar 1444 Bayan Hijira, rana ce da aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki na yini Daya domin jin ra'ayoyin jama'a da kuma tattaunawa akan hanyoyi da matakai domin yiwa kundin tsarin Mulkin kasa gyara da nufin samarda Hukumar Ilimin Almajirci da wadanda zuwa Makaranta baya cikin zabin su a Najeriya (wato Almajiri Education Commission and Out of School Children) Shi dai wannan taro, wanda Hukumar Ilimin larabci da addinin Musulunci ta Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Dr. Umar Aliyu Altine Dandinmahe tareda hadin gwiwar ofishin Maigirma Danmajalisar Wakilai Mai Wakiltar mazabar Bodinga, Dange Shuni da Tureta a karkashin jagorancin Hon. Dr. Balarabe Shehu Kakale da Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) tareda Gidauniyar Shehu Maikoli a karkashin kulawar Hon. Altine Shehu Kajiji ne suka shirya wannan taron tattaunawa na yini daya wanda ya gudana a Babban dakin taro na Hukumar Ilimin larabci da addinin Musulunci ta Jihar Sakkwato. 

Taron yana zuwa ne, bayan wani kudurin doka da Dan majalisar Wakilai Dr Balarabe Shehu Kakale ya gabatar a gaban zauren Majalisa domin neman amincewar  'yan Majalisar Wakilai da kuma al'ummar Najeriya akan duba yiwuwar samarda wannan hukuma. 
Haka kuma taron na yau, yayi tsokaci ne akan abubuwan da suke kunshe a cikin wannan Kudurin doka kamar sassan shi, rabe-rabe, tanade-tanade da kuma muhimman batutuwa dake bukatar ayi fashin baki akansu. 
 
Daga cikin muhimman mutane da suka halarci wannan taro akwai, Maigirma Kwamishinan Ma'aikatar Ilimi matakin farko na Jihar Sakkwato Alhaji Muhammad Bello Abubakar Gwiwa, Shugaban Hukumar Ilimi bai daya ta Jihar Sakkwato Alhaji Altine Shehu Kajiji, Shugaban Kwamitin Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato akan lamurran addini Comrd.Abubakar Shehu Shamaki Yabo, Sarkin Malam Sakkwato, Malam Yahaya Na-Malam Boyi, Babban Liman Masallacin Farfaru Sheikh Abubakar Jibril,Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), Shugaban kungiyar Malamai ta Jihar Sakkwato Sheikh Umar Muhammad Bagarawa, akwai Dokta Ahmad Muhammad Gidadawa (Dangaladiman Waziri), Shugaban kungiyar Alarammomi ta Jihar Sakkwato Imam Muhammad Maigero Dingyadi, Shugaban kungiyar masu Makarantun Allo ta Jihar Sakkwato Sheikh Sidi A. Sidi. Sauran sun hada da Shaihunan Malamai daga Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato: Farfesa Isah Muhammad Maishanu, Farfesa Sani Sagir, Dokta Shadi Sabeh, Dokta Mansur Isah Buhari, Dokta Bashir Muhammad Achida, Shugaban Tsangayar Ilimi a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake nan Sakkwato Dokta Aminu Musa Yabo (Zarumman Yabo da Kilgori),Shugabar kungiyar 'yan uwa Mata Musulmi  Hajiya Amina Sakaba, akwai Limamai daga mazabar Wakilai ta Bodinga,Dange Shuni da Tureta.Akwai Wakilin Gidauniyar Dankade (wato KDC Foundation), akwai wakilan Kungiyoyin kafafen sada zumunta na Takardawa da Rubutaawa (wato Social Media), kungiyar lauyoyi, kungiyar 'yan Jarida ta Kasa reshen Jihar Sakkwato, akwai wakilci daga Hukumar asusun Yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya, wakilci daga kungiyar Lahiya Sak, Babban limamin Garin Yabo, Kungiyoyin Matasa, Alarammomi, hafizzai, Limamai, Ladanai da na ibbai da sauran al'ummar da suka zo daga ciki da wajen Jihar Sakkwato.