Sojojin Najeriya Sun Sha Al'washin Fitowa Da Wasu Sabbin Dabarun Magance Matsalolin Tsaron Da Ke Addabar Kasa

Sojojin Najeriya Sun Sha Al'washin Fitowa Da Wasu Sabbin Dabarun Magance Matsalolin Tsaron Da Ke Addabar Kasa
 

Daga Abbakar Aleeyu Anache,

 

Majalisar tsaron Najeriya ta ce ta yarda kasar na cikin mawuyacin hali inda matsalolin rashin tsaro ya ke cigaba da addabar al'umma, 

 
Wannan dai na daga cikin abububwan da aka tattauna yayin taron majalisar koli ta harkokin tsaron Kasar da aka yi ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari,
 
Wannan dai na zuwa yayin da lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar da har ta kai yan majalisar dattawa daga bangaren adawa kiran da a tsige shugaban kasar, 
 
Da yake wa manema labarai bayani bayan kammala wannan taron mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Manjo-janar Babagana Munguno mai ritaya ya ce majalisar ta amsa cewar kasar na cikin mawuyacin hali,
 
Kuma shugaba Muhammad Buhari ya fahimci irin damuwar da yan kasar ke ciki game da hakan,
 
Muna cikin wani hali mawuyaci matuka kuma majalisa ta fahimci haka, 
 
Shugaban kasa ya fahimci irin damuwar da jama'a ke cikin ga karuwar rashin tsaro, 
 
Na san cewa mutane sun gaji har sun soma karkata ga wasu wuraren domin nemo taimakon yadda za su tsare kansu,
 
Amma gaskiyar al'amari shine taimako kan samu ne kawai idan kowa na taimakon kowa in ji shi,