Gwamnatin Kebbi Ta Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Kwangila Da Kamfanin China Zhonghao

Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Gwamnatin Kebbi dake arewacin Najeriya karkashin jagorancin Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ta sanya hannu kan daftarin yarjejeniyar gina tituna tare da gyara wasu daga cikinsu a garin Yawuri.
Kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Kebbi injiniya Abdullahi Umar Faruk ya ce aikin zai lankwame tsabar kudi har sama da Naira Biliyan 3.
Gwamnatin Kebbi ta sanya hannu kan yarjejeniyar kwangilar gyaran titunan Birnin Yawuri inda za a gyara tituna da nisansu ya kai kilomita biyar da wani abu kan kudi Naira Biliyan Uku da Miliyan Dari takwas da hamsin da hudu da dubu dari biyu da bakwai da Naira biyu da ashirin da tara da kwabo tara.
Kwamishinan ayyukan jihar Kebbi ya ce aikin kwangilar yana daga cikin manufofin gwamnatin jihar na inganta sha’anin samar da ababen more rayuwa a babban birnin jihar da yankunan kananan hukumomin jihar guda 21.