Talauci da rashin shugabanci nagari ne ya haifar da rikici a zanga-zanga a Arewa -- Shettima 

Talauci da rashin shugabanci nagari ne ya haifar da rikici a zanga-zanga a Arewa -- Shettima 

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce rikicin da aka samu yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a yankin Arewa ya faru ne sakamakon talauci da gazawar shugabanci.

Da ya ke jawabi a yayin bikin yaye dalibai a ranar Lahadi, Shettima ya ce dabi'u marasa kyau a yankin Arewa na haifar da kin biyayya ga doka tsakanin matasa.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin mai bashi shawara kan fannin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu za ta gyara tattalin arzikin kasar nan.

Zanga-zangar dai ta kwanaki 10 da aka fara 1 ga watan Agusta ta rikide zuwa rikici a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Shettima ya alakanta hakan ga mahukunta wanda ke da alhakin magance kalubalen da suka shafi al'umma.

"Tsawon lokaci mun bar talauci da cin hanci da shugabanci mara kyau gashi muna ganin sakamako, matasa na tasowa basa girmama dokar kasa da shugabanni",  inji shi.

Shetimma ya ce babu wani dalili da za a bada goyan baya ga satar kayan mutane da sunan zanga-zanga.

Haka kuma, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su bada goyan baya wajen gina kasa.

TheCable