Gwamnatin Taraiya ta gargaɗi ƴan Nijeriya akan furucin da ke ɓata sunan ƙasar
Gwamnatin Taraiya, ta bakin Minsitan Yaɗa Labarai da Tarbiyyar Al'umma, Mohammed Idris ta gargadi ƴan Nijeriya da su guji yin furuce-furuce da ke ɓata sunan ƙasar a idon duniya.
Ya yi wannan gargaɗi ne a wani taro da Cibiyar Horon Hulda da Jama'a, NIPR, ta shirya a Abuja a jiya Talata.
A cewar sa baiyana kyawawan halayen kasa a idon duniya shi ke sanya wa ta samu tagomashi na janyo baki da masu saka hannun jari zuwa ƙasar, inda hakan ke sanya ƙasa ta kara samun ci gaba.
Ya kuma ƙara da cewa bata sunan ƙasa a idon duniya kan janyo ta rasa damammaki na kasuwanci da cigaba.
managarciya