Iyalan Shehu Kangiwa Sun Kokawa Tambuwal Kan Halin Da Suke Ciki
Iyalan tsohon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Shehu Kangiwa sun koka kan halin da suke ciki shekara 40 bayan rasuwarsa, ba wata gwamnati da ta kula a su, abin da yakai ga har yanzu ba a biya su hakkin margayin ba, a lokacin da gwamnonin da ke raye sun ci gajiyar hakkinsu.
A halin da ake ciki gidan da suke ciki yana bukatar a yi masa gyara na musamman domin komai na bukatar canji da shigo da wasu abubuwa na zamani.
A gidan da Muhammadu Shehu Kangiwa gwaman farar hula na farko ya zauna da iyalansa har yanzu a cikinsa suke tare da yara.
An dauki lokaci kafin kafar yada labarai ta 21st CENTURY CHRONICLE ta samu nasarar tattauna da iyalan tsohon gwamna kan shekarru 40 da rasuwar Kangiwa wane hali suke ciki.
Ahmad Shehu Kangiwa Da ne a wurin margayin ya ce mahaifinsu ya bar musu suna mai kyau amma dai bar musu kudi ba suna alfahari da hakan.
Ya ce tun bayan da mahaifinsu ya rasu abin da kawai suke amfana ga gwamnati shi ne abinci a lokacin watan Ramadana da ragunan Sallar layya.
Ya ce har yanzu ba su karbi hakkin mahaifinsu ba tun bayan rasuwarsa, sun tafi ma'aikatar da lamarin ya shafa amma babu biyan bukata 'kan haka muke kira ga Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya shiga cikin lamarin'.
Duk yunƙurin ji daga bakin kwamishinan ma'aikatar Estblishment na jihar Sakkwato Alhaji Sani Bunu Yabo ya ci tura.
Daga Muhammad Nasir.
managarciya