'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Musulunci da Wasu Mutum 30 a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Musulunci da Wasu Mutum 30 a Zamfara

Ƴan bindigan daji sun kai farmaki kauyuka biyu da aka sansu da sana'ar noma a jihar Zamfara kuna sun kashe manoma aƙalla 30.
 
 Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa daga cikin waɗanda ƴan bindigar suka kashe har da babban malamin addinin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun Mai Jan Baki.