Wamakko ya yi ta’azziyar rasuwar jami’an tsaro a Sokoto
Haka ma ya jinjinawa Rundunar Sojoji ta Hadarin Daji kan kokarin da suka yi na mayar da martani ga maharan wannan abin yabawa ne, jajircewarsu ce ta sanya ake samun nasara a yakin da ake da bata-gari da mahara da barayin dajin.
Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattijai Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi ta’aziya ga iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayuwarsu a fagen daga a Sokoto.
Sanatan ya gabatar da sakon ta’aziyarsa a tattanauwar da ya yi da Managarciya kan rashin jami’an tsaron da aka yi a wurin kare al’ummar Sakkwato.
A satin da ya gabata ne Mahara suka yiwa jami’an tsaron kwantan bauna a sansaninsu dake garin Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni a jihar ta Sokoto, in da suka kashe soja 9 da mopol uku da sibil difens 3.
Tsohon Gwamnan ya bayyana bakincikinsa ga wannan lamarin da ya faru na rasa jajirtaccin jami’an tsaro da al’umma ke alfahari da su.
Ya yi addu’ar samun gafarar Allah ga mamatan da baiwa iyalansu hankurin rashinsu.
“Ina mika sakon ta’aziya ta ga iyalan margayan, da danginsu gaba daya Allah ya gafarta masu ya zama gatan abin da suka bari.” A cewarsa.
Haka ma ya jinjinawa Rundunar Sojoji ta Hadarin Daji kan kokarin da suka yi na mayar da martani ga maharan wannan abin yabawa ne, jajircewarsu ce ta sanya ake samun nasara a yakin da ake da bata-gari da mahara da barayin dajin.
Ya kuma jajantawa al’ummar Sabon Birni da Isa da sauran yankunan Sakkwato da ke fama da rashin tsaro da ba su tabbacin kokarin gwamnatin tarayya na ganin ta kawar da rashin tsaro a jihar gaba daya.
managarciya