* Dole A Dakatar Da Zaben Dan Sauraren Hukuncin Kotu- PDP
Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.
Hukumar zabe ta jihar Neja mai zaman kanta ta kara wa'adin kwanaki biyar dan kammala zaben fidda gwani ga yan takarkarun shugabancin kananan hukumomi da kansulolin jihar.
Bayanin hakan na kunshe a wata takardar sanarwar da sakataren hukumar, Ibrahim Mohammed Maburya ya sanyawa hannu littinin din makon nan 19 ga Satumbar 2022. Takardar ta cigaba da cewar duba da wasu jam'iyyu ba su kammala zaben fidda gwani ba, an kara wa'adin kwanaki biyar dan kammala zaben, wadanda suka kammala kuma suka mikawa hukumar sunayen yan takarkarun su zaben su na nan daram.
Bisa tsarin zaben 2002 da aka yiwa gyaran fuska, hukumar na da hurumin gudanar da zabukan kananan hukumomi. Dan haka maimakon gudanar zabukan kananan hukumomi ranar 5 ga watan Nuwambar wannan shekarar, hukumar ta bayyana karin wa'adin kwana biyar inda za ta gudanar da zaben ranar 10 ga watan Nuwambar 2022.
A wata takardar martani ga hukumar da jam'iyyar PDP ta sanar talatar makon nan, 20 ga watan Satumbar nan, wanda shugaban jam'iyyar, Barista Tanko Beji ya sanyawa hannu.
Kamar yadda na sanar da ku, mun tafi kotu dan dakatar hukumar zaben jiha daga gudanar da wannan zaben, a yau lauyoyin mu sun halarci zaman kotun.
Mun shigar da kara a babban kotun tarayya da ke minna, wanda babban lauyan mu Barista Ndayakp SAN ke jagoranta, inda ya bayyanawa kotun shirye shiryen hukumar zaben ba tare da sauraren karar da muka shigar dan sauraren hukuncin kotun ba.
Kotun kamar yadda ta bayyana, ta dakatar da hukumar zaben daga aiwatar da komai dangane da zaben har sai kotun ta saurari karar, duk abinda aka gudanar yanzu rusasshe ne.
A cewar shi wannan shi ne abinda ya faru a kotun a yau talata, kotun ta daukaka zaman zuwa 11 ga watan Oktoban 2022.
Tunda farko dai, kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa ( IPAC) ta bayyana cewar a shirye take dan gudanar da zaben.
A cewarta kungiyar cikin jam'iyyu goma sha shida a jihar, sha biyar sun aminta da zaben, haka yasa wasu jam'iyyu suka gudanar da zaben fidda gwani dan shiga zaben.
Tunda ita PDP ba ta shirya, kuma sabon dokar zaben kananan hukumomi da majalisar dokokin jiha tayi, wa'adin shugabannin kananan hukumomi zai kare cikin watan Disamba, kuma dokar bai amince da nadin rikon kwarya a matakin kananan hukumomi, saboda haka idan PDP
ba ta shirya shiga zaben ba, sauran jam'iyyu sun shirya.