Yadda Bello Turji Ke Nadawa da Sauke Hakimmai  a Sokoto

Yadda Bello Turji Ke Nadawa da Sauke Hakimmai  a Sokoto

  
Shugaban karamar hukuma a jihar Sokoto ya tabbatar da cewa har yanzu wasu yankuna na karkashin ikon yan ta'adda. Shugaban karamar hukumar Isa a jihar, Alhaji Sharifu Kamarawa shi ya tabbatar da haka ga karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle. 
Daily Trust ta ruwaito Kamarawa na cewa dan ta'adda, Bello Turji yana saukewa da kuma daura hakimmai a kauyuka. 
Honarabul Kamarawa ya ce Gabashin Isa an fi samun matsala inda yan ta'adda ke da iko sosai a yankin. 
Hakan ya biyo bayan ziyarar karamin Ministan tsaro jihar Sokoto a kokarin dakile yan ta'addan da suka addabi al'umma. 
"A nan garin Isa muna zaune lafiya amma a Gabashin Isa har yanzu yan bindiga ke da iko inda suke saukewa da nadin dagatai." 
"Mu na rokon jami'an sojoji a sansanin Kagara su kawo dauki a wadannan wurare, a baya muna shi kafin aka dauke shi." - Hon. Kamarawa 
Hon. Kamarawa ya ce tun bayan kisan rikakken dan ta'adda, Halilu Sububu, an dan samu sauki kan hare-haren yan bindiga a yankunan inda ya ce mutane suna yin harkokinsu.