Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri tambuwal ya aminta da kashe wasu kadade a zaman majalisar zartawa da suka yi a satin nan cikin jihar Sakkwato.
A zaman majalisar an aminta da kashe makudan kudi naira biliyan 3.5 domin sake gina hanyar Binji zuwa Silame zuwa Gande, da kuma hanyar Wurno zuwa Huci, da ambaliyar ruwa ta kwashe a kananan hukumomin.
Hanyar Wurno zuwa Huci kasa da sati daya da dan takarar gwamna a jam'iyar APC ya ziyarci karamar hukumar ya yi alkawalin gyara ta a cikin kwana 100 in ya yi nasarar dare kujerar gwamna a zaben 2023, sai gashi majalisar zartawar jiha ta ba da aikin, wanda kammala shi na nufin Tambuwal ya shiga gaban Ahmad Aliyu ta wannan haujin.
Duk da ba a gayyaci manema labarai dake dauko rahoto daga waje ba, a bayanin da gwamnati ta fitar bayan kammala zaman bai bayyana ranar kammala aikin ba, Managarciya na ganin gwamnatin Tambuwal ba za ta yi wargi da aikin ba har a kai ranar zabe domin abokan adawarta na jiran aikin matukar suka samu nasara, kuma hakan na'iya sanya mutanen yankin zabar APC domin aikin kadai, la'akari da yana cikin abubuwan cigaba da karamar hukumar ke bukata.