Ƙungiyar Mata Ta Karrama Malama A Kwalejin Ilmi Ta Gombe

Tace an karrama ta ne a wani taron da kungiyar ta kasa da suka gudanar a Kwalejin Ilimi na gwamnatin Tarayya ta FCE dake Okene, a babban taron ta da ta gudanar. A zantawar ta manema labarai a Gombe bayan wannan  karanci  da aka yi ma ta inda tace tana cike farin cikin, inda ta godewa Allah da kungiyar WICE na yadda suka ga ayyukan Alkairi da take yi har aka mata wannan karamci. Dokta Amina Abdul, ta Kara da cewa an ba ta lambar yabon ne bisa wasu ayyukan taimakon al'umma da jin kai wa marasa galihu musamman 'ya'ya Mata da basu da galihu.

Ƙungiyar Mata Ta Karrama Malama A Kwalejin Ilmi Ta Gombe

Daga Habu Rabeel, Gombe.

Wata Kungiya ta  Mata Malaman  Kwalejin Ilimi ta gwamnatin Tarayya National Association of Women in Colleges of Education (WICE) ta karrama Hajiya Dokta Amina Haruna Abdul Wakiliyar Tula, wacce kwararriyar Malama ce a Kwalejin Ilimi ta gwamnatin Tarayya FCE Gombe da lambar Yabo.

Wakiliyar Tula, tace wannan karanci da  kungiyar WICE tayi mata karramci ne ya sa ta farin ciki domin lambar Yabo nan yabo ne kan  ayyukan jin kai da taimakon al’umma da take yi a ko yaushe wajen ganin ta inganta ilimin 'Ya'ya Mata.

Tace an karrama ta ne a wani taron da kungiyar ta kasa da suka gudanar a Kwalejin Ilimi na gwamnatin Tarayya ta FCE dake Okene, a babban taron ta da ta gudanar.

A zantawar ta manema labarai a Gombe bayan wannan  karanci  da aka yi ma ta inda tace tana cike farin cikin, inda ta godewa Allah da kungiyar WICE na yadda suka ga ayyukan Alkairi da take yi har aka mata wannan karamci.

Dokta Amina Abdul, ta Kara da cewa an ba ta lambar yabon ne bisa wasu ayyukan taimakon al'umma da jin kai wa marasa galihu musamman 'ya'ya Mata da basu da galihu.

 

Har ila yau tace ta dade tana bada guduwar ta wajen ceto rayuwar al’umma musamman a wannan zamani da komai ya tabarbare wajen ganin ta samar wa da Mata yancin su musamman a bangaren samar da ilimin zamani.

   

Sannan tayi amfani da wannan damar tayi kira ga shugabanin  kungiyar su ta WICE da su ci gaba da zakulo wasu matan ana karrama su dan kara musu kwarin guiwa.

 

Daga nan sai tace aikin jin kai Kuma a jinin ta ne Kuma yanzu ne ma ta fara sai lokacin da Allah ya dauki kwanan ta.