Matasa A Neja Sun Goyi Bayan Takarar Tsohon Dan Majalisar Tarayya a APC

Dukkan masu neman wannan matsayin babu kwararre kuma gogaggen da zai iya taka rawar gani kamar Honabul Umar Ahmed Dogon-koli, domin ya shugabanci karamar hukumar Rijau, kuma ya taba wakiltar knanan hukumomin Rijau/Magama a majalisar wakilai ta tarayya, bayan mukaman da ya riqe, wannan na nuna cewar yana da kwarewar da zai rike wannan matsayin idan jam'iyyar APC ta ba shi dama.

Matasa A Neja Sun Goyi Bayan Takarar Tsohon Dan Majalisar Tarayya a APC
Matasa A Neja Sun Goyi Bayan Takarar Tsohon Dan Majalisar Tarayya a APC
Daga Babangida Bisallah, Minna

Matasa a karamar hukumar  Rijau sun bayyana goyon bayan su ga Alhaji Umar Ahmed Dogon-Koli na kujerar sakataren kudin jam'iyyar APC a jihar Neja.

Wannan ya biyo bayan raba muqaman da uwar jam'iyyar ta yi ne dan ganin kowace qaramar hukuma ta samu matsayi dan ba da na ta gudun mawa ga jam'iyyar.

Abdulmajeed Mas'ud, daya daga cikin matasan da suka jagoranci nuna goyon bayan, ya ce su ba girman kujerar suke dubawa ba, suna la'akari da dan siyasar da zai iya taka rawar gani wajen kawo cigaba, hadin kai ga jam'iyyar APC a jihar Neja.
Dukkan masu neman wannan matsayin babu kwararre kuma gogaggen da zai iya taka rawar gani kamar Honabul Umar Ahmed Dogon-koli, domin ya shugabanci karamar hukumar Rijau, kuma ya taba wakiltar knanan hukumomin Rijau/Magama a majalisar wakilai ta tarayya, bayan mukaman da ya riqe, wannan na nuna cewar yana da kwarewar da zai rike wannan matsayin idan jam'iyyar APC ta ba shi dama.
Domin yana da sanayya da hanyoyin da zai bi wajen samarwa jam'iyya kudadeen shiga da zai baiwa jam'iyya damar cigaba da ayyukan da ta sanya a gaba. Mu matasan karamar hukumar Rijau muna neman alfarmar jam'iyyar APC musamman idan an taho zaben shugabannin jam'iyyar a matakin jiha da ta tabbatar ta baiwa Alhaji Umar Ahmed Dogon-Koli wannan damar, muna da tabbacin hakan zai baiwa jam'iyyar kwarin guiwa da samar da shugabanci mai inganci da za ta samar fahimta tsakanin ta da gwamnati mai zuwa.
Da ya juya kan 'yan uwansa matasa kuwa, Abdulmajeed ya bayyana cewar yanzu ne APC ke bukatar matasa ganin gwamnatin tarayya ta amincewa majalisar tarayya yin dokar da ta shafi matasa damar damawa da su a harkokin mulkin kasar nan, saboda haka maganar bangar siyasa ta kare wajibi ne ko wani dan takarar siyasa ya baiwa matasa damar taka rawa saboda a yanzu ne ake bukatar kwarewarsu.
Dangane zaben shugabannin jam'iyya na kasa da jahohi da yankuna kuwa, ya shawarci matasa kar su koma baya su zama a sahun gaba wajen neman dukkanin kujerun shugabancin jam'iyyar.