Gwamnan Bauchi Ya Aje  Mataimakinsa, Ya Dauki Sabon Abokin Takara a 2023

Gwamnan Bauchi Ya Aje  Mataimakinsa, Ya Dauki Sabon Abokin Takara a 2023

 

Gwamnan jihar Bauchi kuma ɗan takarar gwamna a PDP, Bala Muhammed, ya ayyana mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Zaki, Hon. Mohammed Auwal Jatau, a matsayin abokin takararsa na zaɓen 2023.

Honorabul Jatau ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa ɗa ƴan jarida ranar Lahadi a Bauchi, babban burnin jihar ta Bauchi. 
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan mai ci, Baba Kaka Tela, ya rasa damar neman tazarce tare da gwamna Muhammed a babban zaɓen 2023 da ke tafe.
Sabon ɗan takarar mataimakin gwamna ya gode wa mai girma Gwamna Bala Muhammed bisa ganin ya dace da zaɓo shi a matsayin abokin takara a zaɓen 2023. 
Ya kuma tabbatar da cewa zai nuna shi ɗan halak ne kan wannan alafarma ta hanyar zama mataimakin gwamna mai biyayya da goyon baya domin nasarar gwamnatin PDP mai ci a Bauchi. 
"Wannan ba karamar girmama wa bace a gare ni kuma ina mai tabbatar wa gwamna cewa ba zan ba shi kunya kan yakinin da yake da shi a kaina. Ba gwamnatin da ta kyautata kamar ta Ƙauran Bauchi." 
"Baki ɗayan mu mun yi mamakin aikin gwamna ya aiwatar kuma ta yadda mazauna suka dangwali romon demokaraɗiyya babu nuna banbanci, ya zama dole a gare mu, mu tafa wa mai girma gwamna don ya sa mu alfahari." a cewar Jatau