Tambuwal Ya Baiwa Sabbin Kwamishinoni Wurin aiki

Tambuwal Ya Baiwa Sabbin Kwamishinoni Wurin aiki

Tambuwal Ya Baiwa Sabbin Kwamishinoni Wurin aiki
Gwamna  Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto a yau ya baiwa sabbin kwamishinoninsa guda uku.wurin aiki jim kaɗan bayan rantsar da su.
Kwamishinonin sun haɗa da Honarabul Shuaibu Gwanda Gobir,  ma'aikatar albarkatun Ruwa, Honarabul (Prof) Aminu Abubakar, ma'aikatar gona,  Honarabul  Hassan Muhammad  Maccido,  Ma'aikatar aiyukkan cikin gida.

Gwanda zai karɓi aiki ne hannun Honarabul Umar Bature, wanda ya cirata daga kwamishina zuwa sakataren tsare-tsare na ƙasa a jam'iyar PDP.
Sauran kwamishinonin za su maye gurbin Margayi Muhammad Arzika Tureta da Jeli Abubakar.