Sanata Lamido Ya Yi Alhinin Sace Sarkin Gobir Da Wasu Mutum 5

Sanata Lamido Ya Yi Alhinin Sace Sarkin Gobir Da Wasu Mutum 5

Dan majalisar Dattijai mai wakiltar Gabascin Sakkwato Sanata Ibrahim Lamido yayi alhinin sace Sarkin Gobir wanda aka sauyawa wurin aiki zuwa Gatawa da wasu mutum biyar da 'yan bindiga suka yi a karamar hukumar Sabon Birni.

A bayanin da ya fitar a jiha, Sanata Lamido ya nuna bacin ransa kan abin da ya samu wadannan bayin Allah, ya yi fatan kubutar mutanen cikin koshin lafiya.

Sanata Lamido ya jajantawa iyalan mutanen, tare da kara ba su tabbacin cigaba da kokarinsa na ganin an samu tabbataccen tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas.