Kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da jihohin Lagos da Rivers daga karɓar harajin kasuwanci

Wannan yanke hukuncin dai ya biyo bayan karar da hukumar tattara haraji ta Nijeriya FIRS ta shigar kan hukuncin wata kotu da ta bai wa gwamnatin jihar Rivers damar karbar harajin.

Daga Ibrahim Kano

Kotun ɗaukaka kara da ke birnin tarayya Abuja, ta dakatar da gwamnonin jihohin Rivers da Lagos daga karɓar kuɗin harajin kayayyaki da ake kira da VAT.

Alƙalin kotun mai shari’a Haruna Simon Tsanami, ya yanke hukuncin ne a zaman kotun a jiya Juma’a.

Wannan yanke hukuncin dai ya biyo bayan karar da hukumar tattara haraji ta Nijeriya FIRS ta shigar kan hukuncin wata kotu da ta bai wa gwamnatin jihar Rivers damar karbar harajin.

Tun a kwanakin baya ne dai majalisar dokokin jihar Rivers ta amince da dokar karɓar harajin.

A gefe guda kuma yanke hukuncin na zuwa ne sa’o’i kaɗan kafin gwamnan Lagos Babajide Sanwo Olu ya sanya hannu kan dokar.