Ni ne ɗan siyasar da aka fi zagi bayan Tinubu – Wike
Ni ne ɗan siyasar da aka fi zagi bayan Tinubu – Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Cif Nyesom Wike, ya bayyana cewa shi ne ɗan siyasar da aka fi zagi a ƙasar nan, bayan shugaba Bola Tinubu.
Hakan ya zo ne yayin da shugaban hukumar raya yankin kudu maso kudu kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Chibudom Nwuche, ya ce shi da sauran shugabannin siyasa a jihar Rivers za su ci gaba da goyon bayan Wike.
Wike ya jaddada cewa goyon bayansa ga Shugaba Tinubu ya na nan daram, yana mai cewa waɗanda ke ikirarin goyon bayan Shugaban yanzu ba su bayyana a shekarar 2023 ba.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a gidan Nwuche da ke garin Ochigba, a Karamar hukumar Ahoada East ta Jihar Rivers, yayin bikin godiya (thanksgiving) na Shugaban SSDC da iyalansa.
Da yake jawabi ga shugabannin siyasa na karamar hukumar a wata gajeriyar ganawa, Wike ya ce:
“Ba mu taɓa janye goyon bayanmu ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.
“Bari in faɗa muku, bayan Shugaba Bola Tinubu, ni ne ɗan siyasar da aka fi cin mutunci".
managarciya