Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sauke dukkan hafsoshin soja da sufeto-janar na ‘yan sanda, masu ba da shawara, Kwanturola-Janar na hukumar kwastam daga aikinsu da kuma wadanda za su maye gurbinsu nan take.

A sanarwar da Daraktan Yada labarai na ofishin sakataren Gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya sanyawa hannu, ta ce sabbin jami’an da aka nada sune:

1 Mallam Nuhu Ribadu Mai Ba Kasa Shawara Kan Tsaro

2 Manjo Janar C.G Musa Shugaban Hafsan Tsaro

3 Maj. T. A Lagbaja Hafsan Hafsoshin Soja

4 Rear Admirral E. A Ogalla Shugaban Sojojin Ruwa

5 AVM H.B Abubakar Shugaban Hafsan Sojan Sama

6 DIG Kayode Egbetokun Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda

7 Manjo Janar EPA Undiandeye shugaban hukumar leken asiri ta tsaro

Shugaban ya kuma amince da nadin da aka nada:

SAURAN SUNE:

1 Col. Adebisi Onasanya Brigade of Guards Commander

2 Laftanar Kanal Moshood Abiodun Yusuf 7 Guards Battalion, Asokoro, Abuja

3 Laftanar Kanal Auwalu Baba Inuwa 177, Guards Battalion, Keffi, Jihar Nasarawa.

4 Laftanar Kanal Mohammed J. Abdulkarim 102 Guards Battalion, Suleja, Niger

5 Lt. Col. Olumide A. Akingbesote 176 Guards Battalion, Gwagwalada, Abuja

Hakazalika, shugaban ya amince da nadin wasu hafsoshin soji a fadar shugaban kasa kamar haka:

1 Maj. Isa Farouk Audu

(N/14695) Babban Jami’in Yaki da Makamai na Gidan Gwamnati

2 Capt. Kazeem Olalekan Sunmonu (N/16183) Na Biyu a Kwamandan, Makarantun Gidan Gwamnati

3 Maj. Kamaru Koyejo Hamzat (N/14656) Kwamandan hukumar leken asirin soji ta gidan gwamnati.

4 Maj. TS Adeola (N/12860) Kwamandan Rundunar Sojojin Gidan Gwamnati

5 Lt. A. Aminu (N/18578) Na Biyu, Makamai na Gidan Gwamnati

Shugaban ya kuma amince da nadin wasu karin masu ba da shawara na musamman guda biyu (2), da manyan mataimaka biyu (2), wato:

1 Hadiza Bala Usman Mai Bada Shawara ta Musamman, Haɗin Kan Siyasa

2 Hannatu Musa Musawa mai ba da shawara ta musamman kan tattalin arziki da al'adu

3 Sen. Abdullahi Abubakar Gumel Senior Special Assistant , National Assembly Affairs (Senate)

4 Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim Babban Mataimaki na Musamman, Majalisar Wakilai ta Kasa (Majalisar Wakilai)

A karshe shugaban kasar ya amince da nadin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin Mai rikon mukamin Kwanturola Janar na Kwastam.

Idan dai ba a manta ba, manyan hafsoshin tsaron da aka nada da sufeto-Janar na ‘yan sanda da kuma Kwanturolan Hukumar Kwastam za su yi aiki a kan mukamansu, har sai an tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada.