Daga Awwal Umar Kontagora, Minna.
Gwamnatin Neja, ta nemi limaman juma'a da su kara jajircewa wajen yiwa jihar da kasa addu'o'in zaman lafiya ganin irin halin rashin tsaro da tashe tashen hankala da ya addabi kasar. Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan lokacin da sakataren gwamnatin jiha, Hon. Ibrahim Ahmed Matane ya wakilce shi a bude taron yini biyu na karawa juna sani da kungiyar limaman juma'a ta jihar Neja ta shiryawa limamai a babban dakin taro na Legbo Kutigi da ke minna.
Tunda farko gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa na yunkurin farfado da hukumar Hisba da ke yaki da karuwai, da hukumar shari'a da yin sulhun rikicin ma'aurata da rabon gado. Yace hukumomin suna nan daram tun kafa su, ganin yadda fitintinu su kai yawa wanda bisa kiyasi yana da nasaba da irin ayyukan da jama'a ke aiwatarwa na ba daidai ba, dole gwamnati ta dawo da mutane kan turba.
Gwamnan ya bayyana cewar malamai ba abin yarwa ba ne, domin babu gwamnatin da za ta samu nasara ba muddin tayi watsi da malamai, saboda haka gwamnati a shirye take wajen hada guiwa da malamai wajen yiwa kasa addu'a.
A bayaninsa, dan majalisar dattijai mai wakiltar Neja ta tsakiya, Sanata Sani Musa 313 ( Dan Durbin Minna) ya sha alwashin daukar nauyin gudanar da addu'o'in zaman lafiya, wanda ya shawarci limaman da su rika shirya tarukan addu'o'in na musamman a kowani wani wata, domin suna da rawar takawa wajen samun zaman lafiya a kasa.
" Dukkan wadannan matsalolin da ke tasowa musamman na tsarp da ya zamewa al'ummar jihar nan karfen kafa yana da nasaba da sake malamai, saboda haka a shirye na ke wajen yin aiki kafada da kafada malamai dan kai koken mu ga Allah ta hanyar yin addu'o'i da fadakar da jama'a irin gudunmawar da zasu bayar wajen samun zaman lafiya a jihar mu da kasa baki daya.
Ba maganar jam'iyya ba ce, dan APC da PDP da sauran jam'iyyu dukkan su wannan matsalar tsaro tsadar rayuwa ta shafe su, saboda haka mu ajiye maganar siyasa gefe daya mu fuskanci matsalolin da ke damun mu".
Ya kara da cewar ko a majalisar dattijai dukkan dan jihar nan shaida ne akan yekuwa da daga muryar da mu ke yiwa jami'an tsaro na kara jajircewa wajen ganin sun kare rayuka da dukiyoyin jama'ar mu. Musammam yankin da ni ke wakilta a Neja ta tsakiya, da sauran yankunan da wannan matsalar ya rikewa makogoro, ya zama wajibi mu hada hannu dan kawo karshen wannan matsalar.
Da yake karin haske ga wakilin mu, Dakta Umar Faruk Abdullahi, limamin babban masallacin juma'ar Bosso Estate kuma sakataren kungiyar ta jiha, yace kungiyarsu tayi ayyuka da dama na kishin kasa, na janyo hankalin gwamnati da hukumomin da ke shirya jarabawar NAFTEP da WAEC musamman na dakatar da rubuta jarabawar a lokacin sallar juma'a wanda majalisar dattijai ta kasa, da ofishin ministan ilimi sun taka rawar gani akan hakan, ya cigaba da cewar kungiyar mu ta jiha ce ta janyo hankalin NYSC kan yadda take gudanar da ayyukanta a lokacin watan ramadan, wanda wannan ya taimaka gaya na dakatar da atisaye ga mata musulmi a lokacin ramadan.
Mun shirya wannan taron na yini biyu ne ganin zabuka na gabatowa, a karshe mun fitar da matsaya bayan kammala sauraren lakcoci da manyan malamai suka gabatar.
Babban abinda muka mayar da hankali, janyo hankalin iyaye kan kulawa da tarbiyar yara matasa na hana anfani da su lokuttan yakin neman zabe suna shaye shaye a karshe su rika aukawa jama'a.
Sannan mun bayyanawa malamai su jayo hankalin jama'a wajen kaucewa zaben tumun dare, dukkan mun san cancanta kuma duk da cewar ba mu san abinda ke buye ba, amma mun fahimci yan takarkarun da suka dace wadanda muke kyautata zaton alheri akan su.
Taron wanda kungiyar limaman juma'a ( Imam Forum) da gidauniyar Rahama da Bago Foundation suka dauki nauyin shiryawa, ya samu halartar limaman juma'a sama.da dari biyu.
Dan takarar kujerar gwamnan jihar, Hon. Umar Muhammad Bago da mataimakinsa, shugaban jam'iyyar APC.na jiha da wasu daga cikin yan majalisar wakilai da Sanata Sani. musa 313 ( Durbin Minna Karami)suka halarta.