APC Ta Rasa Wani Hazikin Matashi In Da Ya Koma PDP A Sakkwato

APC Ta Rasa Wani Hazikin Matashi In Da Ya Koma PDP A Sakkwato

 

Jam'iyar APC a jihar Sakkwato ta rasa wani hazikin matashi waton Kwamared Nuruddeen Muhammad Mahe in da ya koma PDP domin cigaba da gudanar da siyasarsa.

Jim kadan bayan gwamnan Sakkwato ya karbe shi ya fitar da sanarwar barin jam'iyarsa zuwa PDP in da yake cewa ya bar APC daga yau 18 ga watan Satumban 2022.
"ina sanar da abaokaina da masoyana na yanke shawarar shiga jam'iyar siyasa ta gaskiya, jam'iya mafi girma a Afirika PDP karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal(Matawallen Sakkwato).
"Wannan shawarar ban yanke ta ba rana tsaka, na jima ina bibiyar lamurran dake tafiya a siyasar jihar Sakkwato," a cewar Kwamared.
Ya ce gwamnan Sakkwato jagora ne tabbas, musamman aiyukkan cigaba da ya samar a bangarorin jihar Sakkwato, hankurinsa da sanin yakamatansa ya ishi duk wani mai hankali ya yi tafiya tare da shi.
Mahe ya gode wa duk wasu mutane da ke yi masa fatan alheri a wannan sabuwar tafiyar da ya fara da neman samun nasara.