Hanyoyi Da Dubarun Da'awa: IET Ta Shirya Taron Horaswa Na Kwana Uku
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.
Cibiyar Yada Addinin Musulunci ta kasa Da'awah ta kasa karkashin Jagorancin Shugabanta Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato)
Ta bude taron horaswa akan hanyoyin yin da'awah.
Taron Wanda aka gudanar a cibiyar yada Addinin Musulunci ta IET a Jihar Sokoto.
Ta kaddamar da taron horaswa na Kwanaki ukku
A lokacin da yake jawabi wajen bude taron Shugaban kwamitin Amintattau na cibiyar Malam Muhammad Lawal Maidoki,
Ya yaba tare da janyo hankalin mahalarta taron Akan mayar da hankali ga abinda zasu koya,
ya Kara da cewa duk abinda za a gabatar a lokacin horaswar ba sabon Abu bane illa Karin tunatarwa,
Shugaban ya Kara da bayyana cewa cibiyar ta Jima tana gabatar da irin wannan da'awah ta hannun wadanda suka fara gudanar da ita Kuma duk da yake sun kaura Amma har yanzu cibiyar tana gudanar da ayyukanta a ciki da wajen kasarnan,
Asaboda haka yayi kira ga Al'umma dasu saka hannu wajen ganin cewa an karfafa wannan Al'amari na addinin Musulunci.
Daga karshe shugaban yayi addu'ar samun gafara ga wadanda suka kafa cibiyar har ta Zama yadda yadda ta zama a halin yanzu,
Kamar su Marigayi Sheik Lemu, marigayiya, Aisha lemu, Malam Ashafa da Malam Danjuma Illo.
Shima a nasa jawabi Daraktan Da'awah na cibiyar ta kasa, Kuma shugaban ayarin daga Hidikwatar Cibiyar Dake Minna,
Malam Abdulrahim Sulaiman ya bayyana cewa,
Shekaru hamsin da suka gabata aka fara gabatar da wannan Shirin na da'awah Amma kadan kadan sai da'awar ta fara cigaba har ta kawo yanzu, ya bayyana cewa a wadancan lokuta Ana gudanar da da'awar ce ta wasu bangarorin kasarnan inda maguzawan sukayi yawa kamar Jihar zamfara da kebbi, ya Kara da cewa tun kafuwar da'awar duk inda akaje tana samun karbuwa.
Yace akwai shiraruwa da dama da dabarun da'awah da akebi wajen canzawa wadanda ba Musulmi ba har su karbi addinin Musulunci,
Hakama suna da tsaruka na nunawa matasa hanyoyin dogaro da Kai da Kuma yadda matasa zasu tsara rayuwarsu Domin gobensu.
A jawabansu daban daban Uban Kasar Arkilla Alhaji Aliyu Hassan, da Kwamishinan Lamurran Addini Wanda Daraktan Da'awah na Ma'aikatar Malam Abubakar Umar Darhela ya Wakilta,
Sun yaba yadda aka gudanar tsarin horaswa, tare da Jan hankalin mahalarta taron wajen mayar da hankali akan abubuwan da zasu koya.
Shima a nasa jawabi na Godiya mukaddashin Mai kula da Cibiyar a Jihar Sokoto, Malam Umar Ibrahim Ladan yayi Godiya ya manyan baki da mahalarta taron abisa Gayyatar da suka karba suka halarci taron.
managarciya