Buhari Ya Ba Da Umarnin A Tsige Shugaban APC Mai Mala Buni, A Nada Gwamnan Jihar Neja, A Matsayin Sabon Shugaban Jam'iyyar

Buhari Ya Ba Da Umarnin A Tsige Shugaban APC Mai Mala Buni, A Nada Gwamnan Jihar Neja, A Matsayin Sabon Shugaban Jam'iyyar
Daga Comr Abba Sani Pantami.
Lissafin jam’iyyar APC ya canza yayin da ake zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari da amincewa a sauke Mai Mala Buni daga kan mukaminsa.
Gidan talabijin na Arise TV ta kawo rahoto cewa Mai girma Muhammau Buhari ya yi na’am da a tunbuke Mala Buni daga shugaban APC na rikon kwarya.
A daidai wannan lokaci kuma ya amince da nadin gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa na rikon kwarya.
Wasu gwamnonin APC ake zargin sun kai wa shugaban kasar karan Mala Buni, suka nuna masa cewa bai da shirin gudanar da zaben shugabannin jam’iyya.
Muhammadu Buhari ya karbi maganganun da wadannan gwamnoni su ka kawo, ya bada umarni ayi maza a tunbuke gwamnan Yobe, a maye gurbinsa da wani.
Rahoton ya ce a halin yanzu, gwamnan jihar Yobe watau Mai Mala Buni yana asibiti a Dubai. Hakan ta sa bai samu damar da zai kare kan shi a Aso Villa ba.
Ministan shari’a, Abubakar Malami da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun yi yunkurin sa baki, su hana shugaban kasa daukar wannan mataki.
Masu wannan ra’ayi sun nunawa shugaba Buhari cewa majalisar kolin APC na NEC ce kadai ta ke da hurumin da za tayi waje da shugaban jam’iyya na kasa.
Bugu da kari, ba za a iya tsige Mala Buni kai-tsaye ba sai an sanar da shi na kwanaki bakwai.