Matsalar Ruwan Sha Ta Mamaye Ƙwaryar Birnin Sakkwato
Daga Jabir Ridwan.
A dai-dai lokaci da ake fuskantar matsalar ruwan sha a ajahar sokoto ana ci gaba da samun gaggoriyo wurin samun ruwan sha da tankunan da Gwamnati ta samar ke domin rarraba ruwan sha a wasu sassan birnin Sokoto.
Ana fuskantar karamcin ruwan shan ne a wasu sassan Birnin sokoto sakamakon tsadar man dissel wanda ya yi matukar tashin gwauron zabi abinda yasa masu kwangilar samadddashi suka daina.
Bayanai sun nuna cewa sakamakon karamcin man dissel hukumar samadda ruwan sha ta jahar sokoto ta samadda wasu tankuna da suke bi garka-garka domin saukakawa jamaa.
Jaridar punch ta ruwaito cewa jamaa da dama a unguwar Masallacin Shehu da Kofar Atiku da Sabon Birni da Aliyu Jedo da kuma kofar kade suna ta ruguguwa duk lokacin da tankin ruwan ya isa unguwar.
Wasu kuma sukan yi tururuwa zuwa tashar samadda ruwan sha ta Gwamnatin jahar sokoto da kuma cibiyar rarraba ruwa ta tashar Illela domin samo ruwan da zasu yi amfani da su.
Wata majiya ta shedawa manema labarai cewa, bayaga matsalar tsadar man dissel da sinadaren da ake amfani da su wurin tsabtace ruwan sha akwai wasu basuka da masu kwangilar samadda sinadarai da man ke bi.
Majiyar tace yanzu haka yan kwangilar sun daina samadda dissel da sinadaren tace ruwa.
Duk yake ruwan da mutane ke dibar baa tsabtacesu ba amma hakannan suke ci gaba da amfani da su.
Yayin da wakilin jaridar Punch ya tuntubeshi Babban Manajan hukumar samadda ruwan sha ta jahar Sokoto Alhaji Ismaila Umar Sanda da farko yayi zargin cewa koyaushe yanjarida sun fi bin labarin da aka samu akasi.
Inda yayi zargin Yan jaridar da basa tuntubar hukumar domin jin lamurranta na yau da kullum sai dai in an samu matsala.
Inda ya jaddada cewa dukkanin matsalolin da aka samu masu wucewa ne kuma ana nan ana iya kokari domin shawo kansu.
managarciya