Matsalar Tsaro Za Ta Zama Tarihi Nan Gaba Kadan-----Sanata Wamakko

Matsalar Tsaro Za Ta Zama Tarihi Nan Gaba Kadan-----Sanata Wamakko
 

 

Shugaban Kwamitin tsaro a majalisar dattijan Nijeriya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayar da tabbacin kalubalen tsaro da ake fama da shi a kasar nan zai zama tarihi nan gaba kadan.

Sanata Wamakko ya yi kalaman ne a gidansa dake unguwar Gawon Nama a jihar Sakkwato bayan ya dawo masallacin Idi a mahifarsa dake karamar hukumar Wamakko ya godewa Allah da ya ba  su damar ganin wannan shekara suna cikin koshin lafiya, ya kuma roki Allah ya kawo mafita kan tabarbarewar tattalin arziki da tsadar kayan masarufi da kasar nan ke fuskanta. 
A bayanin da Bashar Abubakar mataimaki na musamman kan yada labarai a kafofin sada zumunta na zamani  ga Sanata Wamakko ya fitar ya ce akwai bukatar musulmai su tashi tsaye ga rokon Allah domin wannan hanyar ce kadai ta rage domin samun mafita a matsalolin da ake ciki, "a roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaron da Nijeriya ke fuskanta". 
Sanata ya godewa magoya bayan jam'iyar APC kan kokarin da suke yi na ganin an samu nasara a kowane mataki ganin zabe na kara karatowa, ya yi kira da su mallaki katin zabe domin shi kadai ne makamin da za su yi amfani da shi wurin zabar shugabanni na gari da suka cancanta, "akwai bukatar gudanar da siyasa ba da gaba ba domin cigaban kasa", a cewar Sanata Wamakko.