Mumunar zanga-zanga ta barke a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo sakamakon halin kunci, tsadar kaya, da kuma rashin takardun Nairan siya ko abinci a Najeriya.
Hotuna da bidiyoyi sun nuna yadda fusatattun matasa sun tare hanyoyi suna kone-konen tayoyi.
TheNation ta ruwaito cewa matasan sun kai hari ofishin gwamnan jihar, Seyi Makinde.
Har direbobin motocin haya ba’a bari a baya ba wajen zanga-zangar.
Halin da talaka ya shiga kan karancin man fetur da naira akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu cikin gagggawa.






