Daga Babangida Bisallah, Minna
Sakamakon ziyarar gani da ido na tantance masu karban fansho a jihar Neja, gwamna Abubakar Sani Bello ya sha alwashin ganin ya biya yan fansho hakkokan su gaba daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyarar bazata da ya kaiwa cibiyar tantance yan fanshon a cikin garin Minna, a Talatar makon nan.
A lokacin ziyarar gwamnan ya zanta da wasu jami'an da ke aikin da wasu masu karban fanshon dan tabbatar da yadda aikin ke gudana a yankunan kananan hukumomi kamar yadda aka tsara.
Da yake zantawa da manema labarai, jim kadan da kammala zagayen, gwamna Sani Bello ya bayyana cewar ya fitar da tsarin tantance yan fanshon ne a yankunan kananan hukumominsu, dan tsaftace aringizon da jami'an fanshon ke yi, yace ba nufi ne na wahalar da yan fanshon ba, shiri ne na tsaftacewa da kaucewa satar kudaden tsoffin ma'aikata da suka kammala shekarun aiki.
"Ba muna nufin yin wannan aikin dan mu kuntata ma wani ba ne, amma ina samun rahotanni yadda yan fansho da dama ba sa samun hakkokansu.
"Da kuma samun rahoton yadda ake aringizo a haujin. Ina sane da irin almundahanar da ake wajen biyan kudin 'yan fansho", a cewarsa.
Ya cigaba da cewa saboda haka, ina baiwa yan fansho hakuri akan yadda ake gudanar da aiki, za mu samu kyakkyawar sakamako.
Gwamnan ya umurci a biya dukkan wadanda aka tantance da kwamitin ta amince da su, wace wadanda suka tsufa ko suna cikin rashin lafiya mai tsanani, su yi hakuri za a same su har gidajen su ko inda suke jinya a tantance su.
Wasu daga cikin 'yan fanshon da wakilin mu ya samu zantawa da su sun bayyana cewar, wannan tantancewar keke da keke da ke gudana zai taimaka wajen zakulo barnar da ake yi da sunan 'yan fansho dan dakile ta.