Uwar Marayu Fatima Maigari  Ta Gudanar Da Bikin Sallah Da 'Ya'yanta A Sakkwato

Uwar Marayu Fatima Maigari  Ta Gudanar Da Bikin Sallah Da 'Ya'yanta A Sakkwato

Daga Aminu Amanawa, a Sakkwato.

Wacce ta assasa gidauniyar Fasaudat Support Foundation Hajiya Fatima Fatima Ahmed Maigari ta shirya liyafar sallah ga marayu da iyayensu a wani mataki na sanya farin ciki ga zukatansu tamkar sauran sauran yara masu iyaye. 

Shugabar Gidauniyar Hajiya Fatima Ahmad Maigari ta bayyana cewa ta shirya liyafar ne domin ganin yara marayu sun gudanar da sallah kamar takwarorinsu masu iyaye.

"Alhamdulillah shekara ta ke wayo, kuma babban abinda ke sani farin ciki a irin wannan lokaci baifi inga yanda yara marayu iri na ke nishadi a irin wannan lokaci, shiyasa nake girmama wannan rana tare kokarin sanya farin ciki a zukatan su".

Hakama Fatima Maigari tayi amfani da wannan damar wajen janyo hankalin wadanda ke rike da marayun kan su kula da amanar da Allah ya dora masu domin amfani al'umma baki daya.

Da yake gabatar da jawabi a wurin liyafar, fitaccen Malamin addinin musulunci Dr. Jabir Sani Maihulla ya kalubalanci shuwagabannin gidauniyar da su sa azukatansu aikin Allah suke gudanarwa domin ribauta a gobe kiyoma.

Ya kara dacewa a dora gidauniyar akan hanyar da koda wadanda ke hidima da kungiya basa raye, gidauniyar zata cigaba a matsayin sadakataul jariya.

Hakama Dr. Jabir Maihulla ya jinjinawa wadda ta assasa gidauniyar akan aikin alkhairi da takeyi ga marayu da marasa karfi, inda yayi kira da ta dore da hakan.

Daga bisani Malam Jabir Sani Maihulla ya bada tallafin naira dubu arba’in a matsayin kudin mota ga iyayen marayun arba’in da suka laharta.